Ephesians 5

1Ku zama masu koyi da Allah, kamar ƙaunatattun ʼyaʼya 2ku kuma yi rayuwar ƙauna, kamar yadda Kiristi ya ƙaunace mu ya kuma ba da kansa dominmu a matsayin sadaka mai ƙanshi da kuma hadaya ga Allah.

3Kada a ma ambaci fasikanci, da kowane irin aikin lalata ko kwaɗayi a tsakaninku, domin bai dace da tsarkaka ba. 4Haka ma bai kamata a sami datti, ƙazamar magana ko zancen banza a cikinku ba, domin ba su dace ba, a maimakon haka sai ku yi ta yin godiya. 5Ku dai tabbata, ba wani fasiki, ko mai aikin lalata, ko mai kwaɗayin (wanda shi da mai bautar gumaka ɗaya ne), da yake da gādo a mulkin Kiristi da na Allah. 6Kada wani yǎ ruɗe ku da kalmomin wofi, gama saboda waɗannan abubuwa ne fushin Allah yake zuwa a kan marasa biyayya. 7Saboda haka kada ku haɗa kai da su. 8Gama a dā zukatanku sun cika da duhu, amma yanzu ku cika da haske daga Ubangiji. Ku yi rayuwa kamar ʼyaʼyan haske 9(domin amfanin haske ya kunshi nagarta, adalci da kuma gaskiya) 10ku nemi abin da zai gamshi Ubangiji. 11Ku yi nesa da ayyukan duhun da mutane suke yi, a maimakon haka, ku tona su. 12Gama abin kunya ne a ma faɗi abubuwan da marasa biyayya suke yi a ɓoye. 13Amma haske zai tona yadda ainihin waɗannan abubuwa suke, 14gama haske ne yake sa kome yǎ bayyana. Shi ya sa aka ce:

“Ka farka, Ya kai mai barci,
ka tashi daga matattu,
Kiristi kuwa zai haskaka ka.”
15Sai ku yi hankali sosai da yadda kuke rayuwa, kada ku yi zama irin na marasa hikima, sai dai kamar masu hikima. 16Ku kuma yi matuƙar amfani da kowane zarafi, don kwanakin mugaye ne. 17Saboda haka kada ku zama wawaye, sai dai ku fahimci ko mene ne nufin Ubangiji. 18Kada ku bugu da ruwan inabi, wanda yake kai ga lalaci. A maimako haka, ku cika da Ruhu. 19Ku yi zance da juna cikin zabura, waƙoƙi da waƙoƙin ruhaniya. Ku rera ku kuma yi kiɗe-kiɗe a zuciyarku ga Ubangiji. 20Kullum ku dinga yin amfani da sunan Ubangijinmu Yesu Kiristi kuna gode wa Allah Uba a ko mene ne.

21Ku yi biyayya da juna saboda bangirmar da kuke yi wa Kiristi.

Mata da Maza

22Matan aure, ku yi biyayya ga mazanku kamar ga Ubangiji. 23Gama miji shi ne kan mace yadda Kiristi yake kai da kuma Mai Ceton ikkilisiya, wadda take jikinsa. 24To, kamar yadda ikkilisiya take biyayya ga Kiristi, haka ma ya kamata mata su yi biyayya ga mazansu cikin kome.

25Maza, ku ƙaunaci matanku, kamar yadda Kiristi ya ƙaunaci ikkilisiya, ya kuma ba da kansa dominta. 26Ya mai da ikkilisiya mai tsarki ta wurin ikon maganarsa, ya kuma tsabtacce ta ta wurin wanke ta da ruwa. 27Kiristi ya yi haka don yǎ miƙa wa kansa ikkilisiya mai ɗaukaka da kuma tsarki, marar aibi, marar tabo ko wani lahani. 28Ta haka, dole maza su ƙaunaci matansu kamar jikunansu. Wanda yake ƙaunar matarsa yana ƙaunar kansa ne. 29Gama ba wanda ya taɓa ƙin jikinsa, sai dai yǎ ciyar da shi, yǎ kuma kula da shi, kamar yadda Kiristi yake yi wa ikkilisiya—  30gama mu gaɓoɓin jikinsa ne. 31“Saboda haka mutum yakan bar mahaifinsa da mahaifiyarsa, yǎ manne wa matarsa, su biyun su zama jiki ɗaya.”
Far 2.24
32Wannan babban asiri ne, amma na ɗauke shi a matsayin kwatanci ne na Kiristi da ikkilisiya. 33Duk da haka, dole kowannenku yǎ ƙaunaci matarsa kamar yadda yake ƙaunar kansa, kuma dole matar ta yi biyayya ga mijinta.

Copyright information for HauSRK